Kila De Gea ya zauna a Old Trafford

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid na son De Gea ya koma Spaniya taka leda

Manchester United na fatan mai tsaron ragarta David De Gea zai ci gaba da zama a Old Trafford.

De Gea bai buga karawar da United ta doke Tottenham a gasar Premier ranar Asabar ba, bayan da Van Gaal ya ce golan yana bukatar natsuwa kan zawarcin da Real Madrid ke yi masa.

United ta dage kan cewar ba za ta sayar wa da Madrid De Gea ba, sai idan Sergio Ramos zai dawo Old Trafford da murza leda.

De Gea ya buga wa United karawar da ta yi da Barcelona da Paris St-Germain a wasannin sada zumunta, amma Sergio Romero ne ya maye gurbinsa a wasan Premier ranar Asabar.

Koci Van Gaal ya ce "Ta yi wu De Gea ya ci gaba da zama a United, amma hankalinsu ba zai kwantaba har sai ranar da aka rufe kasuwar sayen 'yan wasan tamaula ta yanzu".