An ci kwallaye 480 a gasar Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption An buga wasannin mako na 22 a gasar Premier

Bayan da aka buga wasannin mako na 22 a gasar Premier Nigeria ranar Lahadi, an zura kwallaye 480 a raga tun lokacin da aka fara gasar.

Haka kuma alkalan gasar sun bayar da katin gargadi 777, sannan suka sallami 'yan wasa daga fili sau 36.

Kungiyar Enyimba ce ke mataki na daya a kan teburi da maki 41, bayan buga wasanni 22 na gasar, sai Sunshine Stars a mataki na biyu da maki 40, Warri Wolves ta uku da maki 37.

Sharks tana mataki na 17 a kan teburi a sahun 'yan karshe a gasar, yayin da Dolphins ke matsayi na 18, Bayelsa United ce ta 19 sannan Taraba United ta 20 a teburin.

Za a ci gaba da wasannin mako na 23 ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba.