Stoke City na daf da sayen Shaqiri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shaqiri zai koma buga gasar Premier daga Seria A

Stoke City na fatan ta kammala cinikin Xherdan Shaqiri daga Inter Milan a ranar Talata.

Shaqiri dan kwallon Switzerland mai shekaru 23, ya halarci wasan da Liverpool ta doke Stoke City da ci daya mai ban haushi a Britannia Stadium.

Stoke din na son sayen Shaqiri kan kudi £10m, sama da kudin da kulob din ya sayo Peter Crouch daga Tottenham a 2011.

Shaqiri zai zamo dan kwallo na tara da Stoke ta dauka a bana, wata daya bayan tattaunawar da suka fara da Inter ta gamu da tsaiko kan cinikin dan kwallon.

Dan wasan ya koma Italiya da murza leda daga Bayern Munich a watan Janairu, ya kuma ci wa Inter kwallaye 20 a raga.