Xherdan Shaqiri ya koma Stoke City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shaqiri shi ne dan wasa na tara da Stoke ta saya a bana

Stoke City ta kammala sayen Xherdan Shaqiri daga Inter Milan a matsayin dan kwallon da ta saya mafi tsada kan kudi £12m.

Shaqiri dan kwallon Switzerland mai shekaru 23, ya halarci wasan da Liverpool ta doke Stoke City da ci daya mai ban haushi a Britannia Stadium.

Shaqiri ya zama dan kwallo na tara da Stoke ta dauka a bana, wata daya bayan tattaunawar da suka fara da Inter ta gamu da tsaiko kan cinikin dan kwallon.

Dan wasan ya koma Italiya da murza leda daga Bayern Munich a watan Janairu, ya kuma ci wa Inter kwallaye 20 a raga.