Ina tsaka mai wuya a Barca - Pedro

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pedro bai taba buga kwallo a ko ina ba sai Barcelona

Dan kwallon Barcelona Pedro ya bayyana yanayi da yake ciki a kulob din a matsayin "tsaka mai wuya", bayan da wani jami'in kulob din ya ce dan wasan ya bayyana aniyarsa ta bari Nou Camp.

Dan kwallon Spain din mai shekaru 28 wanda ake alakanta shi da Manchester United shi ne ya zura kwallon da ta bai wa Barca din damar lashe kofin Uefa Super Cup.

Barca ta doke Sevilla ne da ci 5 da 4 a wasan da suka buga minti 120.

Kafin wasan jami'in Barcelona, Robert Fernandez ya ce "Pedro na son barinmu."

Amma bayan wasan Pedro ya ce yana cikin fushi saboda ba a soma wasa tare da shi a Barcelona.

Pedro ya zura kwallaye 99 a wasanni 319 a Barcelona inda ya lashe kofunan La Liga biyar da kuma na zakarun Turai uku.