Siasia ya gayyaci 'yan wasa 31 zuwa U-23

Hakkin mallakar hoto Thenff
Image caption Ranar 8 ga watan Satumba za a fara gasar wasannin Afirka karo na 11

Kocin tawagar matasa 'yan kasa da shekaru 23 na Nigeria, Samson Siasia ya gayyaci 'yan wasa 31, domin tunkarar gasar wasannin Afirka da za a yi a Congo Brazzaville.

Tawagar da Siasia ya gayyato ta kunshi yawancin 'yan kwallon da suka buga masa wasannin neman gurbin shiga gasar.

A ranar Laraba ake sa ran dukkan 'yan wasan da aka gayyata za su halarci otal din Parkview da ke Abuja, Nigeria.

Nigeria za ta kara da Ghana da Senegal da Masar a rukuni na biyu na gasar wasannin Afirka da za a fara tsakanin 3-8 ga watan Satumba a Congo, Brazzaville.

Ga sunayen 'yan wasan da Siasia ya gayyata:

Daniel Emmanuel (Enugu Rangers FC); Bala Yusuf Mohammed (Kano Pillars); Erhun Obanor (Abia Warriors); Segun Oduduwa (Nath Boys); Amuzie Stanley (Sampdoria FC, Italy); Azubuike Okechukwu (Bayelsa United); Saviour Godwin (Plateau United); Etebo Oghenekaro (Warri Wolves); Junior Ajayi (3SC); Peter Onyekachi (Enyimba FC); Usman Mohammed (FC Taraba); Atanda Sodiq (Appolonia FC, Albania); Kingsley Sokari (Enyimba FC); Taiwo Awoniyi (Imperial Academy); Chima Akas (Sharks FC); Aminu Umar (Osmanispor FC, Turkey); Daniel Etor (Enyimba FC); Augustine Oladapo (FC IfeanyiUbah); Semiu Liadi (Warri Wolves); Tiongoli Tonbara (Bayelsa United); Ikechukwu Okorie; Etebong Akpan (Club Africain); Sincere Seth (Supreme Court); Abdullahi Shehu (Quadsia FC, Kuwait); Ndifreke Effiong (Abia Warriors); Abiodun Akande (3SC); Dele Alampasu; Lucky Jimoh (36 Lions); Bright Onyedikachi (FC IfeanyiUbah); Olisa Ndah; Solomon Efosa