Southampton na daf da dauko Oriol Romeu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Romeo ya buga wasa aro a Jamus da Spaniya daga Chelsea

Southampton na daf da dauko dan kwallon Chelsea Oriol Romeu domin ya buga mata tamaula.

Romeu mai shekaru 23, ya buga wa Chelsea wasanni 34 tun lokacin da ya koma Stamford Bridge a 2011.

Dan wasan ya ziyarci Southampton ranar Laraba, yayin da tattaunawa ta yi nisa kan batun sayo shi.

Romeu ya buga wasanni aro a Stuttgart ta Jamus da kuma Valencia ta Spaniya.

Dan kwallon ya zauna a kan benci a karawar da Chelsea ta lashe kofin zakarun Turai a 2012, amma baya nan kungiyar ta dauki FA a 2012 da Europa League a 2013.