Mourinho ya sa ba a ga kwazonmu ba — Monk

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jose Mourinho ya ce masu kula da lafiyar 'yan wasansa ba su san harkar kwallo ba.

Kocin Swansea Garry Monk ya ce sukar da Jose Mourinho ya yi wa likitar kungiyar Eva Carneiro, ta janyo ba a maganar kokarin da suka yi na tashi biyu da biyu da Chelsea.

Carneiro ta shigo cikin fili ta duba lafiyar Eden Hazard a kusan karshen wasan abin da ya bar Chelsea da 'yan wasa tara a cikin fili saboda tuni a kai bai wa Thibaut Courtois jan kati.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce masu kula da lafiyar 'yan wasansa ba su san harkar kwallo ba kuma Carneiro za ta rasa mukaminta na lura da lafiyar 'yan kwallo a cikin fili.

"Cece-kuce ya mamaye kokarin da Swansea ta yi. Kafafen yada labarai sun mai da hankali a kan abin da bai kamata ba," in ji Monk.

Monk ya kara da cewa "Kamata ya yi a mai da hankali a kan irin kwazon da muka yi."