Ba za mu sayar da John Stones ba — Martinez

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Martinez ya ce kungiyarsa ba ta sayar da 'yan wasa ba ce.

Kociyan Everton Roberto Martinez ya dage cewa ba za su sayar da dan wasan kungiyar John Stones ga kungiyar Chelsea ba.

Ana sa ran Chelsea za ta sake neman sayen dan wasan mai shekaru 21 a karo na uku bayan an ki sayar da shi a kan £26m.

Martinez ya soki Chelsea bayan da a karon farko ta taya dan wasan a kan £20m.

Da aka tambaye shi a kan ko zai sayar da Stones ranar Alhamis, Martinez ya ce: "Dan wasan ba na sayarwa ba ne, fakat."

Ya kara da cewa: "Matsayinmu a bayyane yake tun daga farko. Mu ba kungiyar ba ce da za ta rika sayar da kwararru 'yan wasanta."

Stones, wanda ya buga wasa sau 23 a gasar Premier ta bara, ya sabunta kwantaragin shekaru biyar da kungiyar a watan Agusta.