'Sakho bai yi ko gezau ba bayan tsare shi'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An tsare Sakho ne bisa zargin cin zarafi.

Kociyan West Ham Slaven Bilic ya ce dan wasan kungiyar Diafra Sakho yana ci gaba da yin atisaye kamar yadda ya saba bayan an tsare shi.

An tsare dan wasan dan kasar Senegal bisa zargin cin zarafi, kwanaki uku kafin wasan da suka doke Arsenal da ci 2-0 na gasar Premier ranar Lahadi a Emirate.

A wani taron manema labarai, Bilic ya ce, "Tabbas na damu [bisa tsarewar da aka yi masa]. Na yi magana da shi, kuma da alama babu abin da ya dame shi. Saboda haka yanzu ina cike da farin ciki".

Bilic ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiya Morgan Amalfitano ba ya cikin jerin 'yan wasan da zai rika sanya wa da farko-farko, sannan ya bayyana dalilin da ya sa West Ham ba ta sayi tsohon dan wasan Ingila, Joey Barton ba.

Ya ce ba su sayi Barton ba ne saboda adawar da masu goyon bayan kungiyar suka nuna a kansa.