Baines zai yi jinyar watanni uku

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jinyar Leighton Baines za ta iya shafar tagomashin Everton

Dan kwallon Everton, Leighton Baines zai yi jinyar watanni uku sakamakon rauni a idon sawunsa.

Dan shekaru 30 da haihuwa, ya ji rauni ne a lokacin horo kafin soma kakar wasa ta bana.

Kocin Everton, Roberto Martinez ya bayyana raunin a matsayin "annoba" ga kulob din.

Ba za a buga wasanni kusan 12 na gasar Premier tare da Baines ciki hadda karawa da Liverpool.

Leighton Baines ba zai buga wasanni Ingila na share fage ba a watan Satumba da kuma Oktoba.