Dan Ghana Daniel Opare ya koma Augsburg

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Opare na jin dadin komawa gasar Bundesliga

Dan kwallon Ghana, Daniel Opare ya koma kungiyar Augsburg ta Jamus daga kungiyar Porto ta Portugal.

Dan wasan mai shekaru 24, ya kulla yarjejeniyar shekaru tare da Augsburg.

Opare ya buga wa Black Stars wasanni 16 kawo yanzu.

Jami'i a kungiyar Augsburg Stefan Reuter ya ce "Daniel matashin dan wasa ne kuma mai kwazo."

Opare ya ce "Na zaku in soma taka leda a gasar Bundesliga."