Villa ta siyo Traore daga Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Traore ya bugawa Spain a matakin 'yan kasa da shekaru 16 da 17 da kuma 19

Aston Villa ta kamalla sayen dan kwallon Barcelona Adama Traore a kan kudin fan miliyan bakwai.

Dan shekaru 19 ya sanya hannu a kwangilar shekaru biyar domin taka leda a Villa Park.

"Dan wasa ne mai kwazo kuma na ji dadin kawo shi nan," in ji kocin Villa Tim Sherwood.

Traore ya buga wa babbar tawagar Barcelona wasanni hudu a yayinda galibin wasansa da karamar tawagar ya ke yi.

Adama Traore ya bi sawun sabbin 'yan wasan da Villa ta siya cike hadda;Jordan Amavi, Jordan Ayew, Mark Bunn, Jose Angel Crespo, Rudy Gestede, Idrissa Gueye, Micah Richards, Scott Sinclair da kuma Jordan Veretout.