Swansea ta doke Newcastle da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gomis ya ci kwallaye biyu daga wasanni biyu da ya buga Premier bana

Swansea ta hada makinta uku a gida, bayan da ta doke Newcastle United da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na biyu da suka kara ranar Asabar.

Janjo Shelvey ne ya bai wa Bafetimbi Gomis kwallo, shi kuma ya zura ta a ragar Newcastle.

Swansea ta kara kwallo ta biyu ta hannun Andre Ayew wanda ya ci da ka, kuma kwallo ta biyu kenan da ya zura tun komawarsa buga gasar Premier.

Newcastle ta kammala karawar da 'yan wasanta 10 a fili, bayan da aka bai wa Daryl Janmaat jan kati, bisa rike Jefferson Montero da ya yi da gangan.

Swansea ta hada maki hudu a wasanni biyu da ta buga, tun farko ta buga 2-2 ne da Chelsea a Stamford Bridge a makwon jiya.