Arsenal ta doke Crystal Palace 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ce ta doke Crystal Palace da ci 2-1 ranar Lahadi

Arsenal ta samu nasara a kan Crystal Palace da ci 2-1 a gasar Premier mako na biyu da suka buga a Selhust Park ranar Lahadi.

Arsenal ta fara wasan da kai matsi a ragar Palace har sai da Olivier Giroud ya ci mata kwallon farko a minti na 16 da fara tamaula.

Minti 12 tsakani da Arsenal ta ci kwallo ne Palace ta farke ta hannun Joel Ward.

Connor Wickham ya buga kwallo ta bugi turke a wasan farko da ya fara yi wa Palace, kuma Damian Delaney ne ya ci gida daga kwallon da Sanchez ya sa mata kai.

Da wannan nasarar Arsenal ta farfado daga doke ta 2-0 da West Ham ta yi a Emirates a makon da ya wuce a gasar Premier wasan farko da suka yi.