Mourinho ya yi wa Arsene Wenger ba'a

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ce ta doke Chelsea a Community Shield

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya yi wa mai horas da Arsenal Arsene Wenger ba'a, a lokacin da yake ganawa da 'yan jaridu kan karawar da zai yi da Manchester City.

Manchester City ta tsawaita zaman kocinta Manuel Pellegrini a Ettihad, bayan da kulob din ya kammala a mataki na biyu a gasar Premier bara.

Da aka tambayi Mourinho ko ya yi mamaki da tsawaita kwantiragin Pellegrini? Sai ya ce "Wa su kungiyoyin suna yin takaicin shekaru 15, amma kuma kocin ne dai yake jan ragamasu".

Rabon da Arsenal ta lashe kofin Premier karkashin jagorancin Wenger tun a 2003-04.

Sai dai kuma Wenger wanda ya fara horas da Arsenal a 1996, ya jagoranci kulob din daukar FA Cup shekaru biyu a jere.

Haka kuma Wenger ya samu nasara a kan Mourinho a karon farko daga wasannin 14 da suka yi a tsakaninsu, lokacin da Arsenal ta lashe Community Shield.