Man City ta lallasa Chelsea da ci 3-0

Image caption Manchester City ta hada maki shida daga wasanni biyu da ta buga

Manchester City ta zazzaga kwallaye uku da nema a ragar Chelsea a gasar Premier wasan makwo na biyu da suka yi a Ettihad.

Sergio Aguero ne ya fara cin kwallo a minti na 31 da fata tamaula, kuma bayan da aka dawo ne daga hutun rabin lokaci kyaftin Vincent Kompany ya ci ta biyu.

Manchester City ta kammala hada makinta uku bayan da Fernandinho ya ci ta uku, kuma maki shida jumulla kenan a karawa biyu da ta yi a gasar.

City ta doke West Brom da ci 3-0 a wasan farko da ta buga a makwon jiya, yayin da Chelsea da Swansea suka tashi 2-2 a Stamford Bridge.

Da wannan sakamakon Manchester City tana mataki na daya a kan teburi da maki shida, yayin da Chelsea ke matsayi na 16 da maki daya kacal.