Athletico Bilbao ta dauki Spanish Super Cup

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan shi ne karo na biyu da Athletico Bilbao ta lashe Super Cup na Spaniya

Athletico Bilbao ta lashe Super Cup na Spaniyar bana, bayan da ta tashi 1-1 da Barcelona a karawar da suka yi a Nou Camp ranar Litinin wasa na biyu.

Barcelona ce ta fara zura kwallo a raga daf da za a tafi hutu ta hannun Lionel Messi.

Athletico Bilbao ta farke kwallon da aka ci ta ta hannun Aritz Aduriz.

Bayan da aka dawo daga hutu alkalin wasa ya bai wa mai tsaron bayan Barca, Gerard Piquejan jan kati, haka ma an kori dan wasan Athletico Kike Sola daga karawar.

A karawar farko da suka buga Athletico ce ta lallasa Barcelona da ci hudu da nema.

Wannan ne karo na biyu da Athletico Bilbao ta dauki kofin Super Cup na Spaniya, yayin da Barca ke da kofin sau 11 da ta lashe a baya.

Hakan ne kuma aka bude labulen da za a fara gasar La liga bana, a inda za a fara wasa ranar Juma'a tsakanin Malaga CF da Sevilla FC.