Mourinho ya fadi dalilin cire Terry a Ettihad

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karon farko da Mourinho ya sauya Terry a wasa

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya fadi dalilin da ya sa ya sauya John Terry a karawar da Manchester City ta doke su 3-0 a gasar Premier ranar Lahadi.

Mourinyo ya sauya Terry da Kurt Zouma tun lokacin da City ta zura musu kwallo daya a raga, kuma karo na farko kenan da kocin ya sauya dan kwallon a lokacin wasa.

Kocin ya tabbatar da cewar Terry bai ji rauni ba, kuma shi ne ya so ya sauya salon kwallon da suke bugawa shi ya sa ya sauya shi.

Mourinho ya kara da cewa "Kawai abin da ya zo min a kaina shi ne ya kamata Zouma ya shiga karawar".

Terry ya lashe kofunan League Hudu da na FA biyar da kofin zakarun Turai da kuma Europa League a tsawon shekaru 17 da ya yi a Stamford Bridge.