Liverpool ta doke Bournemouth 1-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwallon farko kenan da Benteke ya ci wa Liverpool a Premier

Liverpool ta samu nasara a kan Bournemouth da ci daya mai ban haushi a gasar Premier da suka yi a ranar Litinin a Anfield.

Tun farko Bournemouth ta zura kwallo a ragar Liverpool, bayan da Tommy Elphick ya ci da ka amma alkalin wasa ya hana cin kan an yi laifi kafin a ci kwallon.

Benteke ne ya zurawa Liverpool kwallo daga bugun da Jordan Henderson ya yi wo, duk da cewar an nuna a talabijin Philippe Coutinho ya yi satar gida.

Da wannan nasarar da Liverpool ta yi ya sa ta samu maki shida daga wasanni biyu da ta yi, kuma tana mataki na uku da maki 6 a kan teburi.