Jone Stone ba na sayar wa ba ne - Everton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea na son dinke barakar da take fama da ita a bana

Everton ba za ta sallama mai tsaron bayanta John Stone da Chelsea ke son saya ba, har ma ta jaddada cewar ba na sayar wa ba ne.

Kulob din kuma ya ki yin karin bayani kan batun da ake yi cewar bai amince da tayin kudi £30m da Chelsea ta yi wa dan kwallon ba.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho na fatan kara karfin masu tsaron bayansa, bayan da ya sauya John Terry aka kuma doke su 3-0 a gidan Manchester City.

Yanzu ya rage wa Chelsea da Mourinho yanke shawara idan za su kara kudin da suka taya Stone, duk da cewar Everton na kokarin kawo tsaiko kan sayar da dan wasan.