Mourinho ba zai fuskanci tuhumar FA ba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A karon farko Swansea ta samu maki a Stamford Bridge

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ba zai fuskanci hukunci daga hukumar kwallon kafar Ingila ba, kan sukar tawagar likitocin kungiyar da ya yi.

Mourinho ya soki Dr Eva Carneiro da Jon Fearn bisa kai dauki da suka yi wa Eden Hazard a wasan da suka buga 2-2 da Swansea, hakan sai da ya sa dan wasan ya bar cikin fili domin a duba lafiyarsa.

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ce wannan matsalar cikin gida ce, saboda haka su kadai ne za su warware ta.

Mourinho ya kuma tsaya kai da fata kan yadda Carneiro da Fearn suka kai wa Hazard dauki a fili har aka fitar da dan wasan wajen fili a karawa da Swansea ranar 8 ga watan Agusta.

Hakan ne ya kuma sa Chelsea ta karasa fafatawar da 'yan wasa tara a cikin fili, wanda tun farko an bai wa Thibaut Courtois jan kati a wasan.

A karawar da Manchester City ta doke Chelsea 3-0 a ranar Lahadi Chris Hughes ne da kuma Steven Hughes suka maye gurbin Dr Eva Carneiro da kuma Jon Fearn.