Villareal ta kammala daukar Soldado

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Soldado na fatan ya dawo da tagomashinsa a wasannin Spaniya

Roberto Soldado ya bar Tottenham ya koma Villareal da murza leda kan kudi da ake cewa ya kai £7m kan kwantiragin shekaru uku.

Soldado mai shekaru 30, wanda Tottenham ta sayo daga Valencia kan kudi £26m a Agustan 2013, ya ci kwallaye bakwai daga wasannin Premier 52 da ya buga mata.

Dan wasan ya fara murza leda ne a karamar kungiyar Real Madrid, yayin da ya ci kwallaye 63 daga wasanni 120 da ya yi, daga nan ya koma Getafe da Valencia da kuma Tottenham.

Soldado ya buga wa tawagar kwallon kafar Spaniya wasanni 12, kuma komawarsa Spaniya murza leda zai taimaka masa ya dawo da tagomashinsa.