West Brom ta ki sallama Berahino ga Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham na son daukar Berahino zuwa White Hart Lane

West Brom ta ki amincewa da tayin da Tottenham ta yi wa Saido Berahino kan ya koma White Hart Lane da taka leda.

Berahino mai shekaru 22, wanda ya ci kwallaye 20 a wasannin bara, ya buga wa West Brom dukkan wasanni biyu da kungiyar ta yi a Premier bana.

Shugaban West Brom Jeremy Peace ya ce ba su da niyyar sayar da Saido, kuma haka ya shaida wa mai jan ragamar Tottenham Daniel Levy.

Berahino wanda ya ci kwallaye 14 a gasar Premier bara, shi ne dan wasan Ingila na uku a yawan cin kwallaye a gasar, bayan Harry Kane na Tottenham da Charlie Austin na QPR.

Jaridar Daily Telegraph ta ruwaito cewar Tottenham ta taya Berahino kan kudi £15m, wanda kimarsa ta kai £25m.