Romero bai son De Gea ya bar United

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Romero ne ya buga wa United wasan da ta kara da Club Brugge ranar Talata

Mai tsaron ragar Manchester United, Sergio Romero na fatan takwaransa David De Gea ba zai bar taka leda a Old Trafford a bana ba.

Sauran shekara daya kwantiragin De Gea mai shekaru 24, ya kare da United, wanda ake rade-radin zai koma Real Madrid da taka leda.

Romero ya ce De Gea ya na cikin tsaka mai wuya, amma kamar yadda yake kwararren dan kwallo ya kamata ya dinga yin atisaye a kullum domin zai iya buga wa United wasanni.

Kocin United, Louis van Gaal ya yi amfani da Romero a matsayin mai tsaron raga a karawa uku da kungiyar ta yi, a inda ya ce De Gea ya na bukatar natsuwa kan batun komawa Madrid.

Romero ya koma United ne a kakar wasan da aka fara, bayan da kwantiragin da ya kulla a Sampdoria ya kare.