Pedro zai koma Chelsea daga Barca

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pedro ya haskaka sosai a Barcelona

Kungiyar Chelsea ta amince tsakaninta da Barcelona domin sayen dan kwallon Spain, Pedro a kan fan miliyan 21.

Dan shekaru 28 wanda Manchester United ta dade tana zawarcinsa, ana saran zai kama hanyar zuwa London domin a duba lafiyarsa.

Dan kwallon Spain din ya soma ne a karamar tawagar Barcelona kuma tun daga shekarar 2008 da ya soma bugawa babbar tawagar kulob din, ya zura kwallaye 99 cikin wasanni 326.

Pedro zai kasance dan wasa na biyu da Chelsea za ta saya a cikin mako guda bayan sayen dan Ghana Baba Rahman.