United ta taya Sadio Mane na Southampton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man United na fatan kara dauko dan kwallo kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo

Manchester United ta tuntubi Southampton kan ko za ta sayar mata da Sadio Mane dan kwallon tawagar Senegal.

Tun a makwon jiya ne United take ta kokarin karo dauko dan wasa kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa.

Dan kwallon da United ta dade tana zawarci Pedro daga Barcelona ya juya akalarsa a inda yake daf da saka hannu a kungiyar Chelsea.

Mane ya ci kwallaye 10 a wasanni 32 da ya yi a bara a Southampton, tun komawarsa kulob din daga Red Bull Salzburg na Austria kan kudi £10m.