Man City ya sayi Otamendi a kan £32m

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Otamendi yana cikin 'yan kwallo goma sha daya da suka fi haskakawa a gasar La Liga ta 2014-15.

Kulob din Manchester City ya sayi dan wasan gaba na Valencia Nicolas Otamendi a kan £32m.

Otamendi ya sanya hannu a kwantaragin shekaru biyar ne da kulob din.

City zai fara biyan £28.5m a kan dan wasan dan kasar Argentina, wanda ke cikin tawagar zaratan 'yan kwallo goma sha daya wadanda suka fi haskakawa a gasar La Liga ta 2014-15, kuma ya buga wasan karshe na gasar cin kofin Copa America.

Da wasan ya ce, "Abin alfahari ne na kasance a kulob [Manchester City] din da nake kallo daga nesa a matsayin kulob mai ban sha'awa."

Kociyan City Manuel Pellegrini ya ce: "Dan wasan yana da juriya da kwazo, sannan ya iya murza leda."