Bolt ya yi fushi a kan "kwayoyin sa kuzari"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bolt zai fafata da Gatlin a gasar tseren duniya.

Zakaran tseren mita 100 da mita 200, Usain Bolt, ya nuna matukar bakin cikinsa game da yadda aka mayar da hankali a kan masu amfani da kwayoyin kara kuzari a wasan, a daidai lokacin da za a yi gasar tsere ta duniya a birnin Beijing.

Bolt ya shaida wa BBC cewa ba shi kadai ne ke da alhakin dawo da kimar wasan ba.

Dan wasan tseren bai taba fuskantar tuhuma a kan amfani da kwayoyin kara kuzari ba, kuma zai fafata da dan Amurka Justin Gatlin, wanda sau biyu ana dakatar da shi daga shiga tsere saboda amfani da kwayoyin.

Bolt, mai shekaru 28, zai kare kambunsa na tseren mita 100 da mita 200.

Ana sa ran fafatawar ta Bolt da Gatlin za ta yi zafi sosai