Mourinho ne ya ja ra'ayi na - Pedro

Image caption Pedro ya haskaka sosai a Barcelona

Sabon dan kwallon Chelsea, Pedro Rodriguez ya ce kocin tawagar, Jose Mourinho ne ya ja ra'ayinsa ya koma Stamford bridge.

Tsohon dan kwallon Barcelona din, a ranar Alhamis ya koma Chelsea a kan fan miliyan 21.

"Mourinho ya kira a waya sannan ya ce min yanason ya karawa tawagarsa karfi," in ji Pedro.

Dan kwallon Spain din wanda ya lashe kofuna uku na gasar zakarun Turai da kuma na La Liga biyar tare da Barcelona, ana saran a ranar Lahadi zai iya soma bugawa Chelsea a wasanta da West Brom.

Bayanai sun nuna cewar tsohon dan kwallon Barcelona, Cesc Fabregas na cikin wadanda suka ja ra'ayin Pedro.