Kano Pillars za ta fafata da Nasarawa

Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Wasannin makwo na 25 da za a yi ranar Lahadi

Kano Pillars za ta kara da Nasarawa United a gasar Premier Nigeria wasan makwo na 25 ranar Lahadi.

Sauran wasannin da za a buga Lobi Stars za ta karbi bakuncin Ifeanyiubah, yayin da Akwa United za ta kece raini da Giwa FC.

Rangers za ta barje gumi ne da Dolphins a Enugu, a inda Sunshine Stars da El-kanemi Warriors za su kai ruwa rana a Akure.

FC Taraba za ta ziyarci Enyimba a garin Aba, Warri Wolves kuwa za ta fafata ne da Wikki Tourist ta garin Bauchi sai karawa tsakanin Abia Warriors da Heartland.

Ga wasannin makwo na 25 da za a yi ranar Lahadi:

  • Enyimba v FC Taraba
  • Bayelsa United v Sharks
  • Lobi Stars v FC Ifeanyiubah
  • Akwa United v Giwa FC
  • Rangers v Dolphins
  • Sunshine Stars v El-Kanemi
  • Warri Wolves v Wikki
  • Abia Warriors v Heartland
  • Kwara United v Shooting Stars
  • Kano Pillars v Nasarawa United