An karya tarihin kasa doke Kano Pillars a gida

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Twitter
Image caption Sheakaru 12 da kwanaki 44 Kano Pillars ta yi ba a doke ta a gida ba.

Nasarawa United ta kawo karshen tarihin da Kano Pillars ta kafa na yin shekaru 12 da kwanaki 44 ba a doke ta a gida ba a wasan kwallon kafa.

Pillars din ta yi rashin nasara ne da ci 2-1 a hannun Nasarawa United din a gasar Premier wasan mako na 25 da suka buga a ranar Lahadi.

Ubale ne ya fara ci wa Nasarawa United kwallon farko a minti na 12, Bature ya kara ta biyu minti hudu tsakani da kwallon farko da aka ci.

Rabi'u Ali ne ya farke kwallo daya daga cikin wadanda aka ci Kano Pillars.

Ga sakamakon wasannin makwo na 25 da aka buga a ranar Lahadi:

  • Kano Pillars 1-2 Nasarawa Utd
  • Bayelsa Utd 0-1 Sharks
  • Lobi Stars 1-0 FC Ifeanyiubah
  • Akwa Utd 2-2 Giwa FC
  • Rangers 1-1 Dolphins
  • Sunshine Stars 5-0 El-Kanemi
  • Warri Wolves 1-0 Wikki
  • Abia Warriors 1-0 Heartland
  • Kwara Utd 1-0 Shooting Stars