Damben Autan Fafa da Sisco ba kisa

Image caption Bahagon Abba daga Arewa da Shagon Basiru daga Kudu

An ci gaba da wasan damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali zuma dake Dei-Dei a Abuja ranar Lahadi.

Damben farko Shagon Lawan dan Malumfashi ne daga Arewa ya kashe shagon Dan Matawalle daga Kudu a turmin farko.

Sa zare da aka yi tsakanin Bahagon Abba daga Arewa da Shagon Hafsan Kaduna daga Kudu turmi biyu suka yi babu kisa aka raba wasan.

Shagon Ali Mai Maciji daga Kudu kuwa kashe Dogon Jango ya yi daga Arewa, duk da fara wasan Dogon Jango ne ya dumfari Mai Maciji da naushi, amma kuma shi aka kashe a damben.

Sauran wasannin da aka karasa babu kisa musamman wasan Shagon Shagon Alhazai daga Arewa da Shagon Kwarkwada daga Kudu.

Fafatawa ma tsakanin Sarka daga Kudu da Sojan Kyallu daga Arewa babu kisa, haka ma karawa tsakanin Peugeot daga Arewa da Bala kwarkwada daga Kudu.

Shi ma damben Autan Fafa daga Arewa da Bahagon Sisco turmi biyu suka yi aka raba karawar, aka kuma rufe filin da wasa na raha da ya kayatar tsakanin Shagon Bata daga Arewa da kuma Niggan Kudawa kuma babu wanda ya yi nasara a wasan.