Bolt ya lashe tseren mita 100 a Beijing

Image caption Tun farko an yi hasashen cewar Gatlin ne zai lashe tseren

Usain Bolt ya kare kambunsa a tseren mita 100, bayan da ya guje wa Justin Gatlin a gasar wasan tsalle-tsalle da guje-guje da ake yi a Beijing.

Gatlin wanda aka samu da yin amfani da kwayoyi masu kara kuzari sau biyu kuma ana hukunta shi, ya kai wasan karshe ne bayan da ya yi tsere sau 28 babu wanda ya wuce shi.

Bolt din ya kammala tseren ne a dakika 9.79 da hakan ya sa ya lashe lambar zinare, Gatlin kuwa ya karbi lambar Azurfa a matsayi na biyu.

Dan wasan Canada Andre de Grasse da kuma Trayvon Bromell dan Amurka suka karbi lambar tagulla, bayan kare tseren a mataki na uku cikin dakika 9.92.