Arsenal da Liverpool sun tashi canjaras

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal da Liverpool sun raba maki dai-dai a tsakaninsu

Arsenal da Liverpool sun buga canjaras a wasan Premier makwo na uku da suka fafata a Emirates ranar Litinin.

Sau biyu mai tsaron ragar Arsenal Petr Cech yana hana kwallo ta shiga ragarsa da hakan ya hana Liverpool ta samu maki uku a Emirates din.

Philippe Coutinho ya buga kwallo ta bugi turke, yayin da Aaron Ramsey ya zura kwallo a raga amma alkalin wasa ya ce ya yi satar gida.

Alexis Sanchez ma ya buga kwallo ta bugi turke, sannan mai tsaron ragar Liverpool Simon Mignolet ya hana kwallon da Olivier Giroud ya buga shiga raga.

Da wannan sakamakon Arsenal ta hada maki hudu tana kuma mataki na tara a kan teburin Premier, a inda Liverpool take mataki na uku da maki bakwai bayan wasanni uku da suka yi.

Arsenal za ta ziyarci Newcastle ranar Asabar a wasan makwo na hudu a gasar Premier, yayin da Liverpool za ta karbi bakuncin West Ham a Anfield.