'Ana murna idan aka doke Chelsea a wasa'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea za ta karbi bakuncin Crystal Palace a ranar Asabar

Jose Mourinho ya ce lashe wasan farko da Chelsea ta yi a gasar Premier, zai bakanta ran wadanda suke jin dadi idan aka doke ta a wasa.

Chelsea ta samu nasara a gidan West Brom da ci 3-2 a gasar Premier wasan mako na uku da suka kara ranar Lahadi.

A karawar an bai wa John Terry jan kati karo na shida kenan da aka kore shi a wasan Chelsea jumulla, saboda kokarin hana aci kwallo a raga da ya yi.

Nasarar da Chelsea ta samu ta kawo karshen kasa cin wasanni biyu a farkon fara Premier bana, kuma rabon da ta yi hakan tun shekaru 17 da suka wuce.

Chelsea tana da maki hudu a matsayi na tara a kan teburin daga cikin wasannin Premier uku da ta buga, za kuma ta karbi bakuncin Crystal Palace a ranar Asabar 29 ga watan Agusta.