Everton na bukatar dauko 'yan wasa uku

Image caption Roberto Martinez na son kara karfafa karfin Everton a bana

Kocin Everton, Roberto Martinez ya ce yana shirin dauko karin 'yan kwallo uku kafin a rufe kasuwar saye da sayarwar 'yan wasan tamaula ta Turai.

Dan kwallon da Martinez ya sayo Ramiro Funes Mori har yanzu yana jiran takardun izinin buga tamaula a Turai, bai kuma kara a wasan da Manchester City ta doke Everton 2-0 ba.

Everton na tattaunawa da Dynamo Kiev kan batun daukar Andriy Yarmolenko, kuma rahotanni na cewa za ta koma zawarcin Bernard na Shakhtar Donetsk.

Haka kuma kungiyar na son daukar Leandro Rodriguez dan kwallon Uruguay mai shekaru 22 mai taka leda a River Plate.

Martinez ya kuma ce ya dade yana son Manchester United ta bashi aron Adnan Januzaj domin ya murza mata leda.