'Yan wasanmu sun daburce - Benitez

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Wannan ne wasan farko da Benitez ya jagoranci Madrid a gasar La Liga

Kocin Real Madrid, Rafael Benitez ya ce kungiyar ba ta natsu ba kan cin kwallaye a karawar da suka tashi babu ci da Sporting Gijon a gasar La Liga ranar Lahadi.

Madrid wacce Ronaldo da Bale suka buga mata karawar ta kai hare-hare zuwa raga sau 27, amma takwas ne suka nufi ragar kai tsaye.

Haka ma dai Madrid din ta kasa zura kwallaye a raga a wasanni hudu daga cikin karawa takwas da ta yi na gwaji kafin fara gasar bana.

Kocin ya ce sun barar da damarmaki kuma hare-haren da suka dunga kaiwa ba su nufi raga kai tsaye ba.

A gasar La Ligar bana da aka fara an yi karancin zura kwallaye a raga, a inda Barcelona ta samu nasara a gidan Athletico Bilbao da ci daya mai ban haushi.

Ita ma Athletico Madrid wacce ta lashe La Liga a 2014, daya da nema ta ci Las Palmas.