West Brom ta ki sallama Berahino karo na 2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Brom ta dage kan cewar Berahino bana sayar wa ba ne

Kungiyar West Brom taki sallama Saido Berahino karo na biyu da Tottenham ke kokarin sayen dan wasan.

Albion din ba ta sallama tayin da Tottenham ta yi wa Berahino mai shekaru 22 a makwon jiya ba, har ma ta kara da cewar dan kwallon ba na sayarwa ba ne.

Shugaban West Brom, Jeremy Peace ya ce bai sauya batun da ya yi ranar 18 ga watan Agusta ba, inda ya ce ba su da niyyar sayar da Berahino a bana.

Tony Pulis bai saka Berahino a wasan da Chelsea ta doke West Brom da ci 3-2 ba ranar Lahadi, kuma kocin ya ce ya yi hakan ne domin dan kwallon ya samu natsuwa.

West Brom ta sayo 'yan wasa biyu a bana da suka hada da Rickie Lambert daga Liverpool da kuma Salomon Rondon daga Zenit St Petersburg.