Coentrao ya koma murza leda Monaco

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Coentrao zai buga wa Monaco wasanni aro zuwa karshen kakar bana

Mai tsaron bayan Real Madrid, Fabio Coentrao ya koma Monaco da murza leda, a inda zai buga mata wasa aro zuwa karshen kakar bana.

Coentrao dan kwallon Portugal bai samu damar buga wa Madrid wasanni akai-akai ba a bara.

Tsohon kocin Manchester United David Moyes ya yi kokarin ya kai Coentrao Old Trafford domin ya buga mata tamaula a Satumbar 2013.

Dan kwallon mai shekaru 27 ya koma Real Madrid ne daga Benfica a 2011 kan kudi £25m.