Kocin Ghana ya gayyaci Godfred Donsah

Godfred Donsah Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ce gayyata ta farko da aka yi wa Godfred Donsah a tawagar Ghana

Mai horar da tawagar kwallon kafa ta kasar Ghana, Avram Grant, ya gayyaci sabon-yankan-rake Godfred Donsah.

Grant ya gayyaci Donsah ne don ya taka leda a wasan da tawagar ta Ghana za ta buga da Rwanda don neman gurbi a Gasar cin Kofin Kwallon Kafar Afirka ta 2017.

Wannan ne karo na farko da aka kira dan wasan na tsakiya mai shekaru 19, wanda bai jima ba da shiga kungiyar Bologna mai buga wasa a gasar Serie A ta Italiya.

Andre Ayew ma na cikin 'yan wasa 24 da Grant ya gayyata don shiga tawagar; dan wasan na Swansea dai bai samu buga wasan da tawagar ta casa Mauritius a watan Yuni ba.

Ghana da Rwanda, wadanda ke kai-da-kai da maki uku-uku a saman rukunin H, za su kara ne a Kigali ranar 5 ga watan Satumba.

Karin bayani