Nigeria ta yi gaba a gasar kwallon kwado

Hakkin mallakar hoto n
Image caption Ranar Asabar Najeriya za ta kara da Senegal a wasan kusa da na karshe

A ci gaba da gasar wasan kwallon kwando ta nahiyar Afirka da ke gudana a Tunisia, Najeriya da Angola—mai rike da kambun gasar—sun kai zagayen wasan kusa da na karshe.

Bayan ta yi rashin nasara a wasanninta biyu na baya, Angola ta lallasa Masar, yayin da Najeriya ta yi nasara a kan Gabon da ci 87-61.

Kocin Najeriya, Voight, ya ce 'yan wasansa sun gane kura-kuransu kuma za su yi gyara:

"Mun san cewa wasanni biyu na gaba da za mu buga sun fi biyun da muka riga muka buga wahala. Amma ina alfahari da rawar da 'yan wasan suka taka, da kuma yadda inda tawagar ta sa gaba", inji Voight.

Ranar Asabar Najeriya za ta kara da Senegal ko Algeria. Ranar Lahadi ne kuma za a buga wasan karshe, wanda ya yi nasara kuma kai-tsaye zai samu gurbi a gasar Olympics ta badi a Rio de Janeiro kai tsaye.