Kada a sa ni a tawagar I'Coast —Toure

Hakkin mallakar hoto AFP

Dan wasan Manchester City Yaya Toure ya bukaci da kada a saka shi a tawagar 'yan wasan kwallon kafar kasar Ivory a wasan neman gurbin da kasar za ta buga da Saliyo a makon gobe.

Kocin tawagar 'yan wasan Ivory Coast din Michel Dussuyer, ya ce ko da yake Toure na yin nazari mai zurfi a kan makomarsa a harkar kwallo, yana fatan dan wasan zai ci gaba da taka leda tare da 'yan tawagar kasar tasa.

A watan Maris ne dai Toure ya ce yana nazari a kan makomarsa a wasannin kwallon kafa na kasa-da-kasa.

Karin bayani