Markovic zai koma Fenerbace

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lazar Markovic bai haskaka ba sosai a Liverpool

Dan kwallon Liverpool Lazar Markovic, zai koma Fenerbahce a matsayin aro na tsawon shekara guda.

A kakar wasan da ta wuce ne, Markovic ya hade ne da Liverpool a kan fan miliyan 20 a shekara ta 2014.

Dan kwallon Serbia din ya bugawa Liverpool wasanni 34 a kakar wasan da ta wuce.

Shi ma dan kwallon Italiya Mario Balotelli ya bar Liverpool inda ya koma AC Milan a matsayin aro.