Tottenham ta sayi Son daga Leverkusen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Son Heung-min ya haskaka a gasar Bundesliga

Tottenham ta sayi dan kwallon Koriya ta Kudu Son Heung-min daga kungiyar Bayer Leverkusen ta kasar Jamus.

Dan kwallon mai shekaru 23, ya zura kwallaye 29 a wasanni 87.

Yarjejeniyar Son a Tottenham ta kai fan miliyan 22 inda zai kasance tare da Spurs har zuwa shekara ta 2020.

A baya, Tottenham ta nemi sayen Saido Berahino daga West Brom amma kuma aka ki sallama shi.

Son ya bugawa Koriya ta Kudu wasanni 44 inda ya zura kwallaye 11 sannan ya buga gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil a shekara ta 2014.