Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da ziyarta shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a ranar Asabar musamman irin wainar da ake toyawa a nahiyar Turai dama duniya.

06:30 Nan muka kawo karshen shirin tare da fatan za a tara a makwo mai zuwa.

06:27 Wasannin makwo na hudu a gasar Premier Ingila Lahadi 30 ga watan Agusta.

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 01:30 Southampton FC vs Norwich City
 • 04:00 Swansea City vs- Manchester United

06:22 Wasannin Premier Nigeria makwo na 26 Lahadi 30 ga watan Agusta.

 • 04:00 Sharks vs Enyimba
 • 04:00 FC Ifeanyiubah vs Bayelsa Utd
 • 04:00 Giwa FC vs Lobi Stars
 • 04:00 Dolphins vs Akwa Utd
 • 04:00 El-Kanemi vs Rangers
 • 04:00 Wikki vs Sunshine Stars
 • 04:00 Heartland vs Warri Wolves
 • 04:00 Shooting Stars vs Abia Warriors
 • 04:00 Nasarawa Utd vs Kwara Utd
 • 04:00 FC Taraba vs Kano Pillars

06:18 Wasannin Belgium Jupiler League makwo na shida Lahadi 30 ga watan Satumba.

 • 01:30 Club Brugge KV vs Standard de Liege
 • 05:00 KVC Westerlo vs RSC Anderlecht
 • 07:00 KSC Lokeren vs Waasland-Beveren

06:17 Wasannin Portugal SuperLiga makwo na uku Lahadi 30 ga watan Agusta.

 • 04:00 Tondela vs CD NACIONAL FUNCHAL
 • 05:00 Pacos De Ferreira vs FC Arouca
 • 05:00 Sporting Braga vs Boavista FC
 • 07:15 Academica De Coimbra vs Sporting CP

06:15 Wasannin Holland Eredivisie makwo na hudu Lahadi 30 ga watan Agusta.

 • 11:30 Ajax Amsterdam vs ADO Den Haag
 • 01:30 AZ Alkmaar vs Roda JC Kerkrade
 • 01:30 Vitesse Arnhem vs SC Cambuur
 • 03:45 PSV Eindhoven vs Feyenoord Rotterdam

06:13 Wasannin French League makwo na hudu Lahadi 30 ga watan Agusta.

 • 01:00 Saint Etienne vs Bastia
 • 04:00 FC Girondins de Bordeaux vs Nantes
 • 08:00 AS Monaco FCvs Paris Saint-Germain

06:10 Wasannin German Bundesliga makwo na uku Lahadi 30 ga watan Agusta.

 • 02:30 BV Borussia Dortmund vs Hertha Berlin
 • 04:30 SV Werder Bremen vs Borussia Monchengladbach
 • 06:08 Wasannin Serie A makwo na biyu Lahadi 30 ga watan Satumba.
Hakkin mallakar hoto Getty

 • 05:00 AS Roma vs Juventus FC
 • 07:45 Atalanta vs Frosinone Calcio
 • 07:45 AC Chievo Verona vs SS Lazio
 • 07:45 Torino FC vs ACF Fiorentina
 • 07:45 Udinese Calcio vs U.S. Citta di Palermo
 • 07:45 SSC Napoli vs UC Sampdoria
 • 07:45 Genoa CFC vs Hellas Verona FC
 • 07:45 Carpi vs Internazionale

06:00 Za a ci gaba da wasannin Spanish League Primera wasan makwo na biyu Lahadi 30 ga watan Agusta.

 • 05:30 SD Eibar vs Athletic de Bilbao
 • 07:30 Valencia C.F vs Deportivo La Coruna
 • 06:30 Sevilla FC vs Atletico de Madrid
 • 09:30 Las Palmas vs Levante
 • 09:30 Getafe CF vs Granada CF

05:53 West Brom ta amince ta sayi dan kwallon Manchester United, Johnny Evans kan kudi £6m da kuma karin £2m a cikin kunshin yarjejeniya da za su kulla. http://bbc.in/1ErGWST

Hakkin mallakar hoto Getty

05:30 Tottenham vs Everton

Tottenham Hotspur 01 Lloris 02 Walker 04 Alderweireld 05 Vertonghen 03 Rose 15 Dier 08 Mason 19 Dembélé 06 Bentaleb 22 Chadli 10 Kane

'Yan wasan karta kwana: 11 Lamela 13 Vorm 16 Trippier 20 Alli 24 Pritchard 28 Carroll 33 Davies

Everton: 24 Howard 23 Coleman 05 Stones 06 Jagielka 08 Oviedo 16 McCarthy 18 Barry 09 Koné 20 Barkley 15 Cleverley 10 Lukaku

'Yan wasan karta kwana: 01 Robles 11 Mirallas 14 Naismith 17 Besic 19 Deulofeu 27 Browning 38 Pennington

Alkalin wasa: Ref: Mike Jones

05:28 Yanzunnan za a kara tsakanin Tottenham da Everton a wasan Premier makwo na hudu. kuma sun fafata a tsakaninsu sau 167 a dukkan haduwa a tamaula, Tottenham ta lashe wasanni 63, Everton ta ci karawa 54 suka buga canjaras a wasanni 50. Shin wa zai samu nasara a wannan fafatawar?

Hakkin mallakar hoto Getty

05:22 Shin ko an taba yin tunanin Chelsea za ta tsaya a wannan mataki a kan teburi bayan buga wasanni hudu a Premier bana?

05:16 Sakamakon wasannin Bundesliga makwo nauku.

Hakkin mallakar hoto Getty

 • FC Augsburg 0 : 1 FC Ingolstadt 04
 • VfB Stuttgart 1 : 4 Eintracht Frankfurt
 • Darmstadt 0 : 0 TSG Hoffenheim
 • FC Koln 2 : 1 Hamburger SV
 • FSV Mainz 05 3 : 0 Hannover 96

05:12 Sakamakon wasannin Championship na Ingila makwo na biyar.

Hakkin mallakar hoto PA
 • Derby County FC 1 : 2 Leeds United FC
 • Milton Keynes Dons FC 0 : 2 Birmingham City FC
 • Hull City 2 : 0 Preston North End
 • Bristol City FC 1 : 2 Burnley FC
 • Nottingham Forest FC 1 : 2 Cardiff City
 • Huddersfield Town 0 : 1 Queens Park Rangers
 • Rotherham United 1 : 3 Fulham FC
 • Wolverhampton Wanderers FC 2 : 1 Charlton Athletic FC
 • Ipswich Town FC 2 : 3 Brighton & Hove Albion
 • Brentford 1 : 3 Reading FC
 • 1Sheffield Wednesday FC 1 : 3 Middlesbrough

05:01 Sakamakon wasannin Premier da aka buga ranar Asabar

 • Newcastle 0 - 1 Arsena
 • Aston Villa 2 - 2sunderlan
 • Bournemouth 1 - 1leicester
 • Chelsea 1 - 2 Crystal Palace
 • Liverpool 0 - 3 West Ham
 • Man City 2 - 0 watford
 • Stoke 0 - 1 West Brom

04:35 Damben gargajiya yana daga cikin wasannin Hausawa da suka dade suna yi. Kuma wannan takawa ce tsakanin Cindo daga Arewa da Sarka daga Kudu, babu kisa a wannan wasan da suka yi a Abuja, Nigeria.

04:33 Wasannin Belgium Jupiler League makwo na 6.

 • 05:00 OH Leuven vs Sint-Truidense VV
 • 07:00 Mouscron Peruwelz vs Kortrijk
 • 07:00 KV Oostende vs SV Zulte Waregem
 • 07:30 KAA Gent vs KV Mechelen

04:29 Wasannin Portugal SuperLiga makwo na uku

 • Vitoria Sétubal vs Rio Ave FC
 • 06:30 FC Porto vs GD Estoril
 • 08:45 SL Benfica vs Moreirense FC

04:27 Wasannin Holland Eredivisie League makwo na hudu

 • 05:30 FC Utrecht vs FC Groningen
 • 06:45 SBV Excelsior vs De Graafschap
 • 06:45 SC Heerenveen vs PEC Zwolle
 • 07:45 Heracles Almelo vs FC Twente Enschede

04:24 Shin ko kunsan cewar Enyimba ce kan gaba wajen samun fenariti a gasar Premier Nigeria bana, bayan da aka buga wasan makwo na 25 Enyimba ta samu dukan daga kai sai mai tsaron raga sau 8 ta kuma ci 7, sauran kungiyoyi da suka amfana da fenariti a gasar sun hada da Lobi Stars da ta samu 6 sai kuma Akwa United da Kano Pillars wadanda suka samu biyar-biyar kowannensu.

Hakkin mallakar hoto LMGNPFL Twitter

04:15 Sakamakon wasannin Bundesliga makwo na uku da ake buga wa

 • FSV Mainz 05 3 : 0 Hannover 96
 • Darmstadt 0 : 0 TSG Hoffenheim
 • VfB Stuttgart 1 : 3 Eintracht Frankfurt
 • FC Augsburg 0 : 1 FC Ingolstadt 04
 • FC Koln 2 : 1 Hamburger SV

04:12 Usain Bolt ya lashe zinare na 11, bayan da Jamaica ta lashe tseren gudun mita 100 na 'yan wasa hudu na Maza da ake yi a Beijing.

Hakkin mallakar hoto Reuters

04:05 Man City 1-0 Watford Raheem Sterling ne ya ci kwallon

03:37 Sakamakon wasannin Premier da ake fafatawa

Aston Villa 1 : 1 Sunderland Chelsea FC 0 : 0 Crystal Palace FC Bournemouth FC 1 : 0 Leicester City Liverpool 0 : 2 West Ham United Manchester City 0 : 0 Watford Stoke City FC 0 : 0 West Bromwich Albion FC

02:12 Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Salihu Usman Csk: Gani ga wane ya ishi wane tsohttp://topcat2.bbc.co.uk/cgi-bin/topcat2/index.pl#ron Allah liverpool? Dafatan za ku iya tuna abunda ya faru da Arsenal har gida up Man U.

Shu'aibu Idris Kofar-fada Bulangu: Fata Nagari Lamiri, Muna fatan kungiyar kwallon kafa ta Westham tayi wuju-wuju da Liverpool kamar da ci 2-0. Up Gunners.

Sagir Dutse: Aha Liverpool Muna fatan za ku lallasa Westham da ci 3-0 up Arsenal.

Yusuf Nadabo Suleman: Mu yau Man City zamuyi kaca kaca da Watford.

01:04 Jamaica ta lashe Zinare a tseren mita 100 ta mata ta 'yan wasa hudu a cikin dakika 41.07. Amurka ce ta karbi Azurfa a matsayi na biyu sai kuma Trinidad and Tobago ta karbi tagulla bayan da ta kammala tseren a mataki na uku cikin dakika 42.03.

Hakkin mallakar hoto bbc

01:55 Newcastle 0 vs Arsenal 1

01:53 Neymar ya samu sauki daga jinyar da ya yi, har ana sa ran zai iya buga wa Barcelona wasan farko da za ta buga a gasar La Liga da Malaga a Nou Camp. Neymar bai buga wa Barcelona wasan European da kuma Spanish Super Cup ba da kuma karawar da Barca ta doke Athletic Bilbao 1-0 a makwon jiya.

Hakkin mallakar hoto Getty

01:48 An dawo daga Hutu Newcastle 0 vs Arsenal 0

01:47 Wasannin German Bundesliga makwo na uku

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 02:30 VfB Stuttgart -- : -- Eintracht Frankfurt
 • 02:30 FSV Mainz 05 -- : -- Hannover 96
 • 02:30 Darmstadt -- : -- TSG Hoffenheim
 • 02:30 FC Augsburg -- : -- FC Ingolstadt 04
 • 02:30 FC Koln -- : -- Hamburger SV
 • 05:30 Bayern Munich -- : -- Bayer 04 Leverkusen

01:45 Gasar cin kofin Seria A Italiya wasannin makwo na 2

Hakkin mallakar hoto AP
 • 05:00 Bologna FC vs US Sassuolo Calcio
 • 07:45 AC Milan vs Empoli

01:40 Za a ci gaba da wasannin La Ligar Spaniya makwo na biyu

Hakkin mallakar hoto AFP
 • 05:30 Real Sociedad vs Sporting Gijon
 • 07:30 FC Barcelona vs Malaga CF
 • 09:00 Celta de Vigo vs Rayo Vallecano
 • 09:30 Real Madrid CF vs Real Betis

01:36 An je hutu tsakanin Newcastle United vs Arsenal babu ci.

01:32 Mo Farah ya lashe Zinare a tseren mita 5,000 a wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da ake yi a Beijing. Farah wanda ya lashe tseren mita 5,000 da kuma na 10,000 a wasannin Olympics a 2012 ya sake kwata hakan a bana, bayan da ya fara lashe tseren mita 10,000 tun farko a Beijing din. Ndiku ne ya yi na biyu sai kuma Hagos Gebrhiwet a mataki na uku.

Hakkin mallakar hoto Getty

01:21 Likitocin Manchester City na daf da duba koshin lafiyar Kevin de Bruyne a shirin da yake yi na koma can da murza leda. http://bbc.in/1N1Rzyo

Hakkin mallakar hoto Getty

01:03 Newcastle vs Arsenal, an bai wa dan kwallon Newcastle Aleksandar Mitrovic jan kati

12:52 Muhawarar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Salmana Agege: Dafatan yau Chelsea za ta cinye Crystal Palace da ci 4-1.

Basheer Mukhtar: Yusuf Zaria Allah ka ba West Ham nasara a wannan karawa.

Shu'aibu Adam Bagwai: Hahaha, yau za muyi hajijiya da wuju-wuju da West-ham, da ci 3-1.

12:46 An fara wasa tsakanin Newcastle United da Arsenal

12:43 'Yar wasan Belarus Marina Arzamasova ta lashe zinare a tseren mita 800 a gasar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da ake yi a Beijing. Melissa Bishop ce ta Canada ta lashe azurfa a matsayi na biyu sai Eunice Sum a mataki na uku daga Kenya da ta karbi tagulla a tseren.

12:31 Za a ci gaba da gasar English League Div. 1 wato Championship makwo na biyar a yau dinnan

 • Derby County FC vs Leeds United FC
 • Milton Keynes Dons FC vs Birmingham City FC
 • Huddersfield Town vs Queens Park Rangers
 • Wolverhampton Wanderers FC vs Charlton Athletic FC
 • Rotherham United vs Fulham FC
 • Ipswich Town FC vs Brighton & Hove Albion
 • Sheffield Wednesday FC vs Middlesbrough
 • Hull City vs Preston North End
 • Brentford vs Reading FC
 • Nottingham Forest FC vs Cardiff City
 • Bristol City FC vs Burnley FC

12:27 Yau Chelsea za ta karbi bakuncin Crystal Palace a Stamford Bridge, kuma shi ne wasa na 100 da Jose Mourinho zai yi a gida kuma na 200 da zai fafata a Premier. Kocin ya ci wasanni 76 a gida aka doke shi sau daya kacal ya kuma hada maki 250. Kuma Sunderland ce ta doke Chelsea 2-1 a 2014.

12:22 Newcastle United vs Arsenal

Newcastle United: 01 Krul 22 Janmaat 18 Mbemba 02 Coloccini 19 Haidara 04 Colback 08 Anita 20 Thauvin 05 Wijnaldum 07 Sissoko 45 Mitrovic

Masu jiran karta kwana: 09 Cissé 10 de Jong 14 Obertan 17 Pérez 24 Tioté 26 Darlow 27 Taylor

Arsenal: 33 Cech 24 Bellerín 05 Gabriel 06 Koscielny 18 Monreal 34 Coquelin 19 Cazorla 15 Oxlade-Chamberlain 16 Ramsey 17 Sánchez 14 Walcott

Masu jiran karta kwana 02 Debuchy 03 Gibbs 08 Arteta 12 Giroud 13 Ospina 21 Chambers 28 Campbell

Alkalin wasa: Andre Marriner

12:19 Tottenham ta sayi dan kwallon Koriya ta Kudu Son Heung-min daga kungiyar Bayer Leverkusen ta kasar Jamus. http://bbc.in/1NFoitD

Hakkin mallakar hoto Getty

12:15 A ranar Juma a aka kuma raba jadawalin Europa League. http://bbc.in/1fMIxqz

Hakkin mallakar hoto AP

12:13 A ranar Alhamis aka rarraba kungiyoyi zuwa rukuni-rukuni domin fafatawa a zagayen farko na Gasar cin Kofin Zakarun Turai. http://bbc.in/1KsSpCv

Hakkin mallakar hoto AFP

12:10 A shirinmu na sharhi da bayanan gasar Premier kai tsaye za mu kawo muku karawa da za a yi tsakanin Liverpool da West Ham, tare da Aminu Abdulkadir Burci da Aliyu Abdullahi Tanko da kuma Mam'man Skeeper Tw. Za mu fara gabatar da shirin da karfe 2:30 agogon Nigeria da Niger. Za kuma ki iya bayar da gudunmawa ko tafka muhawara a lokacin da ake gabatar da shirin.

Hakkin mallakar hoto Reuters

12:05 Za a fara karawa tsakanin Newcastle da Arsenal a filin wasa na St Jame's Park

Hakkin mallakar hoto Getty

Newcastle da Arsenal sun kara a dukkan haduwa a wasannin tamaula sau 176, Newcastle ta samu nasara a fafatawa 66, Arsenal ta ci wasanni 72 sannan suka yi canjaras sau 38

12:00 Za a ci gaba da gasar Premier wasannin makwo na hudu a yau dinnan, ga kuma karawar da za a yi

 • Newcastle United FC vs Arsenal FC
 • Chelsea FC vs Crystal Palace FC
 • Liverpool vs- West Ham United
 • Bournemouth FC vs Leicester City
 • Aston Villa vs Sunderland
 • Manchester City vs Watford
 • Stoke City FC vs West Bromwich Albion FC
 • Tottenham Hotspur vs Everton FC