West Brom ta dauki Johnny Evans

Image caption Louis van Gaal ba ya saka Evans a wasannin United

West Brom ta amince ta sayi dan kwallon Manchester United, Johnny Evans kan kudi £6m da kuma karin £2m a cikin kunshin yarjejeniya da za su kulla.

Evans mai shekaru 27 zai ziyarci Midland a ranar Asabar, kuma ana sa ran za su kammala cimma yarjejeniya a karshen makwonnan.

Dan wasan ya buga wa United wasanni 198, ya kuma lashe kofunan Premier uku a Old Trafford.

Evans zai buga tamaula a West Brom tare da Darren Fletcher wanda ya bar United a watan Janairu, kuma aka nada shi kyaftin a West Brom din.

A watan Maris aka dakatar da Evans daga buga wasanni shida, bayan da aka same shi da laifin tofawa Papiss Cisse yawu na Newcastle.