Wolfsburg ta dauki Dante na Munich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dante ne ya bukaci ya bar Munich ganin ba a saka shi a wasanni

Wolfsburg ta amince ta sayi mai tsaron bayan Bayern Munich, Dante, amma ba ta fayyace kudin da za ta dauko dan kwallon ba.

Dante dan wasan Brazil wanda ya buga wa tawagar kasar wasanni 13, ya kuma lashe kofunan Bundesliga uku da kofin zakarun Turai kafin a dai na sa shi a wasa akai-akai.

Shugaban Bayern Karl-Heinz Rummenigge ya ce Dante ne yake son ya dunga buga wasa a koda yaushe, mu kuma ba za mu hana shi wannan damar da ya samu ba.

Dante mai shekaru 31 zai saka hannu kan yarjejeniyar shekaru uku da Wolfsburg a ranar Litinin.