Wikki Tourist ta doke Sunshine Stars 2-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Wasannin makwo na 26 da aka buga a gasar Premier Nigeria

Wikki Tourist ta samu nasara a kan Sunshine Stars da ci 2-1 a gasar Premier Nigeria wasan mako na 26 da suka yi a ranar Lahadi.

Victor Yakubu ne ya fara ci wa Wikki kwallo a minti na 13 da fara wasa, Mubarak Umar ya kara ta biyu minti uku tsakani.

Sauran wasannin da aka buga Sharks da Enyimba sun tashi wasa Canjaras, Nasarawa United ta doke Kwara United da ci 3-0.

El-Kanemi Warriors kuwa tashi wasa 2-2 ta yi da Enugu Rangers, Giwa FC kwallaye 2-0 ta ci Lobi Stars, sai Kano Pillars da ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a Taraba.

Ga sakamakwon wasannin makwo na 26 da aka buga.

  • Sharks 0-0 Enyimba
  • FC Ifeanyiubah 1-0 Bayelsa Utd
  • Giwa FC 2-0 Lobi Stars
  • Dolphins 2-0 Akwa Utd
  • El-Kanemi 2-2 Rangers
  • Wikki 2-1 Sunshine Stars
  • Heartland 1-0 Warri Wolves
  • Shooting Stars 2-0 Abia Warriors
  • Nasarawa Utd 3-0 Kwara Utd
  • FC Taraba 1-0 Kano Pillars