Swansea ta doke Manchester United 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta yi wasanni uku a jere a gasar Premier kwallo ba ta shiga ragarta ba

Swansea ta doke Manchester United da ci 2-1 a gasar Premier wasan makwo na hudu da suka kara ranar Lahadi.

Juan Mata ne ya fara zura kwallo a ragar Swansea minti na 48 da fara tamaula

Sabon dan wasan da Swansea ta sayo Andrew Ayew ne ya farke kwallon da aka zura musu a minti na 61.

Ayew ne dai ya bai wa Gomis kwallon da ya ci United ta biyu a karawar, kuma karo na uku da Swansea ta doke Manchester United a jere kenan.

Haka kuma Swansea ta zama kungiya ta shida da ta doke United karo uku a jere, sannan a lokacin da Louis van Gaal ke bikin yin wasa na 50 a United din.

Swansea za ta ziyarci Watford a wasan makwo na biyar, yayin da Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool a Old Trafford.